Wata babbar kotu da ke Kaduna ta yanke hukuncin mayar da jagoran kungiyar mabiya shi’a IMN Sheikh Ibraheem El-Zakzaky da matarsa gidan yari, bayan lauyoyinsa sun ce an hana su izinin ganawa da shi daga hannun hukumar tsaro ta farin kaya DSS.
Kotun ta yanke hukunci ne a safiyar yau Alhamis, inda ta ce za a mayar da su gidan yarin ne don lauyoyinsu da likitocinsu su samu damar ganinsu cikin sauki.
Lauyan El-Zakzaky da matarsa Zeenatu, Femi Falana SAN wanda Barista Haruna Magashi ya wakilta ya ce an hana su gana da su ne tun bayan dawowarsu daga kasar Indiya.