✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ba PDP iznin sanya sunayen shaidu a karar zaben Gwamnan Kano

Kotun daukaka kara da ke Kaduna ta ba Jam’iyyar PDP iznin shigar da sunayen shaidu cikin kunshin takardar korafin da ta shigar gaban kotun sauraren…

Kotun daukaka kara da ke Kaduna ta ba Jam’iyyar PDP iznin shigar da sunayen shaidu cikin kunshin takardar korafin da ta shigar gaban kotun sauraren kararrakin zabe da ke zama a Jihar Kano.

Kotun ta bayar da wannan izni ne bisa rokon da dan takarar Gwaman a karkashin tutar Jam’iyyar PDP Injiniya Abba K. Yusuf da Jam’iyyarsa ta PDP suka yi a gabanta inda suka kalubalanci hukuncin kotun sauraren kararrakin zaben Gwamnan Jihar Kano akan batun.

Idan za a iya tunawa makonni biyu da suka gabata kotun sauraren karrarkin zaben karkashin jagoranci Mai shari’a Halima Shamaki ita ta yanke hukunci cewa Jam’iyyar ta PDP da dan takararta ba su da damar kara sanya sunayen wasu shaidu a cikin kunshin takardar karar wanda suka riga suka bayar tun da fari.

Sai dai yayin da take yanke wancan hukunci kotun daukaka karar karkashin jagorancin Mai shari’a Misis A.O Okogie ta kafa hujja da cewa Jam’iyyar PDP za ta iya shigar da jerin sunayen mutanen duba da cewa tun da farko ta shigar da shaidar da mutanen suka bayar cikin kunshin takardar karar don haka sanya sunansu a yanzu bai kaucewa ka’ida ba.

Sai dai Jam’iyyar APC da Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje sun sha alwashin tafiya kotun koli don kalubalantar wannan hukunci na kotun daukaka karar.