Search
Subscribe
Kotu ta bayar da belin ‘Mama Boko Haram’ Naira Miliyan 30

Kotu ta bayar da belin ‘Mama Boko Haram’ Naira Miliyan 30

A yau Laraba bayan da Hukumar yaki da cin hanci EFCC ta gurfanar da Barista Aisha Alkali Wakil, wadda ake yi wa lakabi da Mama Boko Haram da wasu mutum uku, a gaban kotu bisa zargin laifin zambar kudi Naira miliyan 62.

Shari’a Aisha Kumaliya ce ta babbar kotun jihar Borno ta jagoranci shari’ar a yau Laraba, inda ake zarginsu da laifuka har uku.

Bayan zaman kotun an bayar da belin Aisha Alkali Wakili kan kudi Naira milyan 30, amma saboda rashin halartar wadanda ake zargin kotun ta ce za ta dage bayar da belin.

Barista Aisha Alkali Wakil ta taka rawa yayin tattaunawar sulhu tsakanin kungiyar Boko Haram da gwamnatin Najeriya, abin da ya sa ake yi mata lakabi da ‘Mama Boko Haram’.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin