✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta bayar da umarni rufe tashoshin talabijin din da ke yada shirye-shiryen Aljazeera a Masar

Wata kotu a Masar ta bayar da umarnin rufe tashoshin talabijin da ke yada shirye-shiryen Aljazeeera, a wani shirin gwamnatin kasar na toshe kafofin yada…

Wata kotu a Masar ta bayar da umarnin rufe tashoshin talabijin da ke yada shirye-shiryen Aljazeeera, a wani shirin gwamnatin kasar na toshe kafofin yada labarai da ke nuna goyon bayansu ga kungiyar ’Yan uwa Musulmi, da hambararren shugaban kasar, Muhammad Mursi.
A wata takaddamar shari’a, kotun soja ta bayar da umarnin daurin rai da rai a kan magoya bayan Mursi, inda ta daure wani shekara 15, tare da wasu mutum 51, wadanda ake tuhuma da cin mutuncin sojojin kwantar da tarzoma a birnin Suez.
Magoya bayan Mursi, suna amfani da kafafen yada labarai, saboda ba su ga wata kafa da ke nuna za a sasanta da su ba. Ita kuwa gwamnatin kasar na zargin Aljazeera da yi mata zagon kasa, inda take nuna hotunan baya, sabanin hakikanin abin da ke aukuwa.
Gidan talabijin na Aljazeera ya karyata zargin da gwamnatin Masar a karkashin jagorancin soja ke yi mata. Kuma akwai wakilansu biyu da aka daure, daya daga Al-Jazeera Mubasher Misr, saura ukun da ke daure sun fito ne daga wasu tashoshin da ke yada shirye-shiryen Aljazeera. Har yanzu dai ana  yada shirye-shiryen Aljazeera Mubasher Misr.
Shaimaa Abu ElKhir, shugaban kwamitin bayar da kariya ga ’yan jarida a birnin Alkahira, ya ce hukumomi na amfani da tunzurawar a matsayin dalilin da ya sa suke gurfanar da tashoshin talabijin, duk da cewa babu wata doka da ta yi bayani kan abin da ake nufi da “tunzurawa.”