✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ce a rataye wanda ya kashe ’yar tsohon Mataimakin Gwamnan Ondo

A shekaranjiya Laraba ce Babbar Kotun Jihar Ondo da Akure ta yanke wa Adeyemi Seidu hukuncin kisa ta hanyar ratayewa saboda samunsa laifin kashe budurwarsa,…

A shekaranjiya Laraba ce Babbar Kotun Jihar Ondo da Akure ta yanke wa Adeyemi Seidu hukuncin kisa ta hanyar ratayewa saboda samunsa laifin kashe budurwarsa, Khadija Oluboyo, wanda ’yar tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Ondo Alhaji Lasisi Oluboyo ce.

Ana zargin Adeyemi ya kashe Khadijat a gidansu ne a watan Yulin bara, kuma an ruwaito cewa bayan ya kashe ta, sai ya binne gawarta a cikin dakinsa har kwana biyar, kafin daga baya mahaifinsa ya gane,  ya tona abin da ya faru ta hanyar kai karar dan ga  ’yan sanda.

Ana zargin Adeyemi ya kashe Khadijat, wadda take karatu a Jami’ar Adekunle Ajasin ce da nufin yin asiri.

Bayan an gabatar da shi a kotu, Adeyemi ya bayyana cewa ba shi ne ya kashe Khadijat ba, inda ya ce wadansu abokansa ne suka aikata wannan mummunan aiki.

Daya daga cikin shaidun da aka gabatar a kotun, Dokta Olumuyiwa Pelemo wanda ya binciki gawar, ya tabbatar da cewa bincikensu ya nuna cewa ta ji raunuka da yawa kafin ta mutu, sannan an yanki gashin kanta da na gabanta.

Shi ma kanen wanda ake zargin ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce wansa ya bukaci ya nemo masa buhun da zai sa gawar Khadijat, amma ya ki.

Mahaifin wanda ake zargi, Seidu Siyanbola wanda magini ne, ya tabbatar da labarin karamin dansa, inda ya ce ya san cewa dansa Adeyemi na soyayya da Khadijat na kusan shekara uku.

Ya kara da cewa Adeyemi ya tabbatar  masa cewa wai wadansu abokansa sun kashe Khadijat, sun binne ta a dakinsa.

Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Samuel Bola ya ce an tabbatar da cewa lallai kashe Khadijat aka yi kuma da gangan, don haka ya yanke hukuncin kisa ta hanyar ratayewa ga Adeyemi Seidu.