✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ci gaba da sauraron karar ma’aikatan NTI 150 da aka dakatar

Kotun Harkokin Ma’aikata ta Kasa (National Industrial Court) da ke Abuja, ta ci gaba da sauraron karar da wadansu mutum 150 suka shigar agabanta, kan…

Kotun Harkokin Ma’aikata ta Kasa (National Industrial Court) da ke Abuja, ta ci gaba da sauraron karar da wadansu mutum 150 suka shigar agabanta, kan dakatar da shirin daukarsu aiki a Cibiyar Horar da Malamai ta Kasa (NTI) da ke Kaduna ta yi, wata uku bayan sun fara aiki a cibiyar a shekarar 2016.

Ci gaba da sauraron shari’ar wanda ya gudana a ranar Litinin da ta gabata, an sake daga shi zuwa ranar 20 ga Fabrairu, bayan fara zama a ranar da alkalin kotun Mai shari’a Sanusi Kado ya jagoranta.

Masu korafin wadanda cibiyar ta dauke su aiki a lokacin tsohon Babban Daraktanta, Dokta Aminu Ladan Sharehu, sun yi korafin cewa an dakatar da shirin daukarsu a matsayin cikakkun ma’aikata ne bayan umarnin haka daga jagororin hukumar na yanzu, kamar yadda takardun bayani da lauyansu Barista Muhammad Sani ya gabatar ga kotun a madadinsu, suka nuna.

Sun ce sun cika dukan ka’idojin daukar aiki kamar rajista da Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa (NIHS) da rajistar zama mamba a kungiyar fansho ta Najeriya, sannan an kai ga ba da lambar ma’aikaci na ma’aikatar ga kowannensu, inji bayanin.

Haka sun ce kimanin mutum 30 daga cikinsu an kai ga sanya su a tsarin kundin bayanai na biyan ma’aikata albashi, (IPPIS), lokacin da umarnin dakatarwar ya zo ba tare da an yi musu wani bayani ba. Kuma sakamakon hakan ne suka garzaya kotun don ta bi masu kadi, kamar yadda takardun korafin nasu da suka gabatar ga kotun suka nuna.