Search
Subscribe
Kotu ta ci Neymar tara saboda saba yarjejeniyarsa da Barcelona

Dan wasan gaba na kungiyar PSG, Neymar Jnr.

Kotu ta ci Neymar tara saboda saba yarjejeniyarsa da Barcelona

Kotu ta umarci dan wasan gaba na PSG, Neymar ya biya tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona Yuro miliyan shida da dubu dari bakwai bayan ta yi watsi da korafin da dan wasan ya gabatar a kan Barcelona.

Tun bayan sauya shekarsa zuwa PSG a kan yarjejeniya mafi tsada a duniya, Neymar ya yi karar kungiyar Barcelona yana neman ta biya shi sama da Yuro miliyan 43 a matsayin alawus-alawus.

Yayin yanke hukunci a kan karar, alkalin kotun ya yi watsi da bukatar Neymar, ya kuma amince da bukatar kungiyar Barcelona da ita ma ta yi karar dan wasan bisa saba ka’idojin kwantiraginsa.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ta ruwaito cewa, kotun ta ba wa Neymar shekaru biyar ya daukaka kara.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin