Kotu ta dage sauraron shari’ar Oscar Pistorous da ya kashe budurwarsa

Kotun majistare da ke Afirka ta Kudu ta roki menama labara na kasar da kuma na waje da su daina yin riga-malam-masallaci wajen yada labaran shari’ar dan tseren guragun kasar da ake zargi da kashe budurwarsa mai suna Reeba Steenkamp a watan Fabarairun da ya wuce.
Kotun ta ce yadda wasu kafofin watsa labaran kasar ke rige-rigen buga labarin don sayar da jarida  bai dace ba don akwai yiwuwar su yada abin da ba haka yake ba.  Asalima kotun ta ce a shari’ar da aka fara yi wa Oscar a ranar Litinin da ta gabata tuni Lauyoyin da ke gabatar da kara suka nemi kotun da ta ba su isasshen lokaci don cigaba da gudanar da bincike.
A kan haka kotun ta ce tuni ta dage sauraron karar zuwa watan Agusta mai zuwa inda ake sa ran cigaba da sauraron karar.
Ana zargin Oscar Pistorious wanda ke da nakasa a hannu da kafa kuma yake wakiltar kasar a gasar tseren nakasassu (Paralympic)  da laifin dirka wa budurwasa bindiga da ya yi sanadiyyar ajalinta ba tare da saninsa ba.
An ce dan tseren nakasassun wanda ya lashe wa kasar Afirka ta Kudu lambar zinare sau shida a gasar wasanni ta Olamfik daban-daban ya dirka wa budurwar tasa harasahi ne a watan Fabrairun da ya wuce a tsammaninsa barawo ne ya yi masa shigar burtu.
Bayan ya fito daga ban daki ne ya tarar da abin da ya faru daga nan jami’an tsaro suka yi awon gaba da shi.
A watannin baya ne aka bayar da belinsa kuma sai a wannan lokaci kotu ta fara sauraron karar.
Yanzu dai kotu ta dage karar sai watan Agusta idan Allah Ya kaimu.