Search
Subscribe
Kotu ta daure direba kan zargin yi wa agolarsa ciki a Abuja

Kotu ta daure direba kan zargin yi wa agolarsa ciki a Abuja

Wata Kotun lardi ta birnin tarayya da ke Garin Jiwa Abuja, ta bada umarnin tsare wani direba mai shekara 36 mai suna Samson Boje, kan zargin yi wa agolarsa ciki, bayan rasuwar mahaifiyarta.

Lauya daga sashin shigar da kara na gwamnatin tarayya mai suna Uche Uchegbulam, a yayin shigar da karar a yau Litinin ya shaidawa kotun cewa, bayan rasuwar mahaifin yarinyar, mahaifiyarta ta auri mutumin, amma sai itama Allah Ya karbi rayuwarta a watan Disamba ta shekara ta 2013.

Ya ce, a watan Yuni na wannan shekarar, yarinyar ta taso daga gidan wani baffanta inda ta ke da zama a wani yanki na Abuja don ziyartar kanwarta mai shekara 6 da mahaifiyarta ta haifa a gidan wanda ake zargin, amma sai ya shaida mata cewa yarinyar bata nan, sai dai ta sake dawo wa, kamar yadda ya yi bayani.

Sai dai a cewarsa bayan yarinyar ta sake komawa gidan sai mutumin ya riketa sannan a qarshe ya yi mata fyade da ya kaita ga samun ciki da ke da wata 4 a yanzu, in ji lauyan.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin