Daily Trust Aminiya - Kotu ta daure lauya shekara 7 a Kalaba
Subscribe

Kotu ta daure lauya shekara 7 a Kalaba

Babbar kotun Tarayya da ke Kalaba a jihar Kuros Riba, ta yanke hukuncin dauri na shekaru bakwai a kan wani babban lauya, Ezechi Okereke, sakamakon samun sa da laifin aikata zamba cikin aminci.

A ranar Juma’ar da ta gabata ce kotun ta yanke hukunci kan karar mai lamba FHC/CA/ CR/33/2015 tsakanin wanda ake tuhuma da wanda ya shigar da karar tun a shekarar 2015, Enwono Abasi Emmanuel Eyo.

Okereke ya karbi tsabar kudi daga hannun Enwono Eyo da yarjejeniyar zai bashi takardun mallakar wani fili a unguwa mai alfarma ta Satelite da ke birnin Kalaba, lamarin da ya kasa cika alkawari.

Alkalin da ya jagoranci zaman kotun Mai shari’a I.E. Ekwo, ya ce hukuncin daurin ya fara tun daga ranar 8 ga watan Yulin 2015, lokacin da aka kawo karar sa kotun.

Alkalin ya ce kotu ta samu wanda ake tuhuma Ezechi Okereke da laifin aikata zamba cikin aminci sakamakon damfarar Emmanuel Eyo, wanda hakan ya sabawa sashe na 13(a) (b), 2 da 3 cikin dokokin aikata miyagun laifuka.

Hakazalika Mai shari’a Ekwo ya umarci lauya Okereke ya biya Emmanuel kudinsa naira 2,955,000 kafin a sake shi.

texem
More Stories