Kotu ta daure lauyan bogi shekara uku

Kotu ta yanke wa wani lauyan bogi, Adedeji Ebenezer Oluwagbenga hukuncin daurin shekara uku a gidan yari. 
A ranar 5 ga watan Agustan 2020 ‘yan sanda suka kama Adedeji Ebeneza a lokacin da yake tsaka da aiki a kotun Majistare da ke zamanta a Itori a Abeokuta, Jihar Ogun.
A ranar 12 ga watan Agusta lauyan bogin da ake tuhuma ya gurfana a gaban alkalin  kotun Mai Shari’a B.A Somorin wanda ya tabbatar da laifin na yin aiki ba bisa ka’ida ba da sunan lauya a kotu alhali yana sane shi ba lauya ba ne.
Da farko wanda ake tuhumar ya ki ya amsa laifin, kafin daga bisani ya amsa bayan da aka gabatar da shaidu a kansa.
Nan take alkalin kotun ya yanke masa hukuncin daurin shekara uku a gidan yari tare da aiki mai tsanani, ba tare da zabin tara ba.