✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure manajan banki shekaru biyu a kurkuku

Babbar kotun Jihar Kano ta yanke wa wani tsohon manaja na daya daga cikin rassan tsohon bankin Ocenic wanda a yau ya zama bankin Ecobank…

Babbar kotun Jihar Kano ta yanke wa wani tsohon manaja na daya daga cikin rassan tsohon bankin Ocenic wanda a yau ya zama bankin Ecobank hukuncin daurin shekaru biyu a gidan kurkuku a kan zargin almundahanar wasu kudade har Naira miliyan 65.
Shi dai wannan tsohon manajan mai suna Usman Salifu an zarge shi ne da satar kudi har Naira miliyan 65 daga ma’ajiyar wani mutum mai suna Yusuf Saleh Dunari a wannan bankin.
A farkon lokacin da aka gurfanar da shi a gaban kotun manajna bai amsa laifuka guda hudu da ake zarginsa da shi ba, sai a zaman kotun na ranar Litinin din da ta gabata sannan ya amsa wadansu daga cikin laifukan.
Lauyoyin wanda ake karar sun nemi kotu ta yi masa sauki wajen yanke masa hukunci saboda shekarunsa da kuma irin nauyin da ke kansa na iyali.
Sai dai mai gabatar da kara, Muhammad M. Gambo daga Hukumar Yaki da Almundahanar Kudade (EFCC) ya nemi kotu ta yanke wa wanda ake zargin hukunci mai tsauri ta hanyar daure shi a gidan kaso.
Da take yanke hukunci game da laifi na farko, mai shari’a Dijeh Aboki ta yanke wa wanda ake zargin, wanda a yanzu haka aka kore shi daga aiki, hukunci daurin watanni shida ko kuma biyan tarar Naira miliyan biyu. A game da laifi na biyu da na uku shi ma an yanke wa wanda ake zargin daurin watanni shida-shida  ko kuma biyan tarar Niara dubu 500. A game da laifi na hudu wanda yake shi ne na karshe an yanke wa wanda ake zargin hukuncin daurin watanni hudu ko kuma biyan tarar Naira dubu 500.
Sannan a karshe kotun ta umarci wanda ake zargin ya mayar wa mai kara kudinsa Naira miliyan 65.