✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure matashi kan aikewa da hotunan batsa ga mutane

Babbar Kotun Tarayya da ke Ibadan ta yanke hukuncin daurin shekara daya a gidan yari ga wani matashi mai suna Ismail Yunus kan samunsa da…

Babbar Kotun Tarayya da ke Ibadan ta yanke hukuncin daurin shekara daya a gidan yari ga wani matashi mai suna Ismail Yunus kan samunsa da laifin yin amfani da na’urar kwamfuta ’yar yawo (laptop) wajen aikewa da sakon hotunan batsa ga wadansu mutane da ya damfare su kudade. Da take yanke hukuncin Alkalin Kotun, Mai shari’a Joyce Abdulmalik, ta bayar da umarnin kwace na’urori da kayayyakin da mai laifin ya yi amfani da su wadanda aka gabatar a matsayin shaida a gaban kotu a mika wa Gwamnatin Tarayya.

Haka Alkalin Kotun ta umarci mai laifin ya mayar da jimlar  Dalar Amurka 410 (kusan Naira dubu 150) ga mutanen da ya damfara ta hanyar aike musu bidiyo da hotunan batsa a cikin na’urorinsu.

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa ce ta gurfanar da matashin a gaban kotu bayan kama shi kan zargin aikata laifin wanda ya saba wa sashe na 24 (1) (a) na dokar hana yin amfani da na’urorin kwamfuta  wajen aikata miyagun ayyuka ta shekarar 2015, wadda ta yi tanadin irin wannan hukunci.

Kafin a yanke masa hukunci sai da Ismail Yunus, ya amince da aikata laifin da aka tuhume shi da shi.