Aminiya

Kotu ta daure matashi rai-da-rai kan kashe mahaifinsa a Akwa Ibom

Gwamna Ben Ayade na Jihar Kuros Riba

Wata Babbar Kotu da ke Karamar Hukumar Ibiono Ibom a Jihar Akwa Ibom, a zaman da ta yi ranar Larabar makon jiya ta yanke wa wani matashi mai suna Utube Ita, hukuncin daurin rai-da-rai  sakamakon samunsa da laifin kashe mahaifinsa mai suna Oscar Ita. Kotun a hujjar da ta bayar na yanke wa matashin hukuncin daurin shi ne bayanin da wanda ake zargi Utube, ya yi wa ’yan sanda a ofishinsu lokacin da suka kama shi, inda ya shaida musu shi ya kashe mahaifinsa ba tare da wani ne ya tilasta masa ba. Kotun ta nuna gamsuwa da bayanan da ta samu daga hannun ’yan sandan cewa, shi ne ya kashe mahaifinsa. Matashin ya bayyana wa kotun cewa, sun samu sabani ne da mahaifinsa, shi kuma ya kashe shi.

Da yake yanke hukunci Mai shari’a Bassey Nkanang, ya ce an kawo wanda ake zargin kotu ne bisa zargin farko da aka yi masa na aikata laifin kisan mahaifinsa wanda ya saba wa  dsashe na 326 [1] na dokokin aikata miyagun laifuffuka, kundi na 38 littafi na 2 na dokar Jihar Akwa Ibom na shekara ta 2000 mai lambar caji HIT/3C/2018 wanda ya yi nuni da laifin kashe mutum ba gaira babu dalili.

Dan uwan Oscar Ita, mai suna Godwin Udoisang, da yake bayar da shaida a kotun ya ce, tsakanin 5 zuwa 11 ga watan Yunin 2017 sun nemi Oscar Ita, ba su ganshi ba sun  bincika ko’ina a karkara ba su gan shi ba, babu kuma labarinsa ko inda aka ce an gan shi sun bincika har makwabta amma babu labarin ganinsa ko jin duriyarsa.

Udoissang, ya ci gaba da cewa, “Lokacin da na tambayi Utube ina mahaifinsa ya shiga? Sai ya ce, shi fa bai  gan shi ba bai kuma san inda ya shiga ba.

“Hankalinmu ya tashi amma kuma ba mu natsu ba sai na yanke shawarar bincikar gidan da dan uwana yake tare da dan nasa Utube muna cikin bincike sai muka ga tarin kasa, muka tone sai muka ga ai dan uwana ne da muke nema kwana da kwanaki ba mu gan shi ba, an kashe shi an binne,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Daga nan ne muka sanar da Sashen Binciken Manyan Laifuffuka na Rundunar ’Yan sandan Jihar da ke Ikot Akpan Abiya, muka je da mai  daukar hoto bayan mun tone gawar aka dauki hoton gawar nan ne muka ga wanda ake zargi da kisan kan ya binne gawar da takalmin dan uwana kafar hagu.

Babban Lauyan Jihar Mista O. P. Okpo, ya ce  duk da kasancewa, babu wasu kwararran shaidun gani da ido da za su tabbatar da lokacin da aka yi kisan kan amma mun gamsu da furucin da wanda ake zargi da kisan ya yi ga ’yan sanda na cewa shi ne wanda ya kashe mahaifinsa.

A nasa bangare lauyan da ke kare wanda ake zargi Lawrence S Udonwa ya ce, tunda babu shaidun gani da ido mutum hudu da za su bayar da shaida kan abin da wanda ake zargi ya aikata don haka hukuncin da kotu ta yanke ta yi shi ba bisa ka’ida ba, bai kuma dace da wanda aka yanke wa hukuncin ba.

Ya kara da cewa, hotuna da mai daukar hoto ya yi da rahoton da dan sanda mai gabatar da kara ya kai gaban kotu tunda su ba kwararru ba ne hakan ya saba da sashi na 1 da na 3 na doka na hotunan da aka nuna, wanda wadannan duk ba su isa a yarda da su a matsayin wata hujja da kotu za ta dogara da su har ta yanke hukunci ba.

Mai shari’a Bassey Nkanang, ya dogara da hujjar da tasa aka  yanke hukuncin kuma hukuncin da aka yanke ya nuna  kotu ta gamsu da duk hujjojin da aka gabatar mata, na sai da aka  samu yamutsi a tsakanin wanda ya kashe da kuma wanda aka kashe. Sannan alkalin ya ce, “Kotu ta gamsu da hujjojin da aka gabatar mata, hakika wanda ake zargi shaida ne da aka gabatar ta tababtar da cewa, wanda ake zargin shi ne ya yi kisan don haka kotu ta yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai.”