✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure tsohon ma’aikacin banki shekara 10 saboda satar kudin abokan huldar bankin

Alkalin Babbar Kotun Jihar Ekiti, Mai shari’a Abiodun Adesodun ya zartar da hukuncin daurin shekara 10 a gidan yari ga wani tsohon ma’aikacin Bankin Fidelity…

Alkalin Babbar Kotun Jihar Ekiti, Mai shari’a Abiodun Adesodun ya zartar da hukuncin daurin shekara 10 a gidan yari ga wani tsohon ma’aikacin Bankin Fidelity na garin Ado Ekiti mai suna Michael Adedayo Ihinolurinjon saboda samunsa da laifin sace Naira miliyan 8 da dubu 891 mallakar abokan huldar bankin da suka ajiye a cikin asusunsu ta hannun wannan mutum.                                                                                                                                                       Ofishin Hukumar Yaki da Yi Wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) na Ibadan ne ya gurfanar da Michael Adebayo gaban kotun. Kakakin Hukumar EFCC Mista Tony Orilade ya fadi a cikin wata takardar sanarwa cewa binciken da suka yi na baya-bayan nan ya nuna cewa Michael Adebayo ya karkatar da akalar wadannan kudi mallakar masu hulda da bankin daga asusun ajiyarsu a bankin zuwa  aljihunsa ne ta haramtacciyar hanya. Takardar shaida da Bankin Fidelity ya gabatar a gaban kotun ta nuna cewa tsohon ma’aikacin bankin ya sace kudin ne a cikin mako uku na farkon watan Satumban  shekarar 2016, inda ya rika yin layar zana daga kan kujerar da yake aiki idan ya hango abokan huldar bankin da suka shigar da kudi ta hannunsa.                                                                                                                                                    Lauyan Hukumar EFCC, Abdulrasheed Lanre Suleiman ya gabatar da shaidu mutum  tara tare da gabatar da wasu takardu a matsayin shaid aa gaban kotun domin tabbatar da wannan laifi.

Bayan sauraron karar ce, Mai shari’a Abiodun Adesodun ya amince da tuhuma biyu da ake yi wa Michael Adedayo, inda ya yanke masa hukuncin daurin shekara 5 a kan kowane laifi tare da ba shi zabin biyan tarar Naira dubu 100 a kan kowane hukunci tare kuma da biyan Naira miliyan 7 ga bankin na Fidelity.