✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure tsohon Shugaban NIMASA shekara 42

Mai Shari’a Mojisola Olatorengun ta Babbar Kotun Tarayya da ke a Jihar Legas ta yanke wa tsohon shugaban riko na Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen…

Mai Shari’a Mojisola Olatorengun ta Babbar Kotun Tarayya da ke a Jihar Legas ta yanke wa tsohon shugaban riko na Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa  (NIMASA) Mista Calitus Obi daurin shekara 42 a gidan kaso tare da Mista Alu Dismas wanda yake Mataimaki ne ga Obi da kuma  Mista Akpobolokemi.

Mai shari’ar ya same su ne da laifi dumu-dumu wanda ya kunshi caji na biyu da na ukku da na hudu da na shida da na bakwai da na takwas, wanda kowanne laifi da irin nasa hukuncin.

Haka zalika Mai Shari’ar ya ba shi zabin tarar Naira Miliyan 42 a kan kowane caji   wanda ya kama Naira miliyan 252 ke nan a jimilla. Sannan  masu laifi na biyu  da na ukku kuma tarar Naira miliyan 10.

Wadanda aka yanke wa hukuncin ana tsare da su ne tun watan Disambar  2016  yayin da ake tuhumar su da laifuka  8.   Daga cikin laifuffukan akwai hada baki da kuma karkatar da kudade ta barauniyar hanya  da cin hanci da rashawa na Naira miliyan 136.

Dukannin wadanda ake tuhuma an same su da laifi.

A yayin gudanar da shari’ar an gabatar da shaidun mutum takwas (8) da kuma wadansu takardu da suke dauke da shaidar aikata laifin.

Lauyan masu shigar da kara ya bukaci  a yanke musu hukunci mai tsauri, ba tare da yin la’akari da sashi na 270, wanda hakan zai takaita bata lokaci.

Sannan kuma ya bukaci kotun ta umurce su da su dawo da kudeden da suka sace ga Hukumar NIMASA sannan su biya ta diyya.