✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure wanda ya sace rufin coci a Osogbo

Kotun Majistare ta Osogbo a Jihar Osun, ta yanke hukuncin daurin wata 8 a gidan kaso ga wani mai suna Ganiyu Wakili da ta same…

Kotun Majistare ta Osogbo a Jihar Osun, ta yanke hukuncin daurin wata 8 a gidan kaso ga wani mai suna Ganiyu Wakili da ta same shi da laifin satar kwanukan rufi da kudinsu ya kai Naira dubu 80 mallakar cocin Life Oasis International.

Da yake yanke hukunci kan laifin a ranar Talata da ta gabata, Alkalin Kotun Mai shari’a Opeyemi Badmus, ya ce ya gamsu da bayanan da mai gabatar da kara Mista Olayiwola Rasak ya yi  ga kotun cewa Ganiyu Wakili ya aikata laifin da ake tuhumarsa a ranar 5 ga Janairun da muke ciki.

Mai gabatar da karar ya ce, mai gadin cocin ne ya kama mai laifin da misalin karfe 9:30 na dare a ranar. Ya ce, akwai wani mutum mai suna Azeez Ayomide, mai shekara 17 da wani daban da ya tsere da aka kama su tare da Ganiyu Wakili lokacin da suke kwasar kwanukan rufi daga wajen da aka ajiye su a cikin cocin. Ya ce, laifin ya saba wa sashi na 516 da 390 na dokokin Final-kod sashe na na kundin dokokin Jihar Osun na shekarar 2002.

Da yake bayyana wa kotun dalilin aikata wannan laifi, Ganiyu Wakili, ya amince da satar wadannan kaya inda ya ce  matsin rayuwa ce ta jefa shi aikata laifin. Amma ya roki kotun ta yi masa sassauci wajen yanke hukunci musamman saboda kasancewarsa magidanci mai iyali.

Alkali Opeyemi Badmus, ya bayar da umarnin mika Azeez Ayomide ga kotun kananan yara saboda karancin shekarunsa a yayin da ya yanke hukuncin daurin wata 8 ga Ganiyu Wakili ba tare da zabin biyan tara ba.

A wani bangaren kuma wata matar aure mai suna Rukayyat Adekunle ta shaida wa Kotun Gargajiya ta Oja-Oba Mapo a Ibadan cewa, mijinta mai suna Kamarudeen Adekunle, ya yi karyar cewa ta tsare shi da makami a hannu tana kokarin hallaka shi. Matar ta ce, “Mijina ya yi wa kotu karyar cewa, na rike makami a hannu  ina kokarin hallaka shi alhali ba haka muka yi da shi ba. Gaskiyar abin da ya auku a tsakaninmu shi ne an samu matsalar kasa daukar nauyin abinci da kudin makarantar ’ya’yanmu biyu da kula da lafiyarmu inda na nuna rashin amincewa da irin wannan zama. Maimakon daukar matakin sasanta tsakaninmu sai ya kulle ni ya kama dukana ba gaira ba dalili, sai da na kubutar da kaina daga duka ta gatsa masa cizo a kunne. Wannan ne ya sa yake yi min kazafin cewa ina rike da makamin da nake so in kashe shi.”

Rukayyat, wacce ta kai karar mijinta ta roki kotun ta raba aurensu domin a cewarta ya saba hulda da ’yan banga da ke tayar da hankalin mutane a cikin unguwarsu. “Kuma na taba yin belinsa daga hannun ’yan sanda bayan sun kama shi a dalilin irin wannan hargitsi da suka saba yi,” inji ta.

Ta ce, duk kokarin da ta yi wajen kai karar mijinta ga iyayensa domin sasantawa ya ci tura domin a kowane lokaci suna goyon bayansa ne.

Da yake kare kansa, Kamarudeen ya ce, “Ni ma ina so kotun ta raba auren namu domin fitinar matar tawa ta ishe ni. Gaskiya ta fadi cewa ina zaman rashin aikin yi, inda take taimakona wajen daukar dawainiyar gida, amma karya ta yi cewa, ita ce ta yi belina a lokacin da ’yan sanda suka kama ni. Wannan ko kusa ba a yi haka ba, sharri ne irin nata,” inji shi.

Bayan sauraron bangarorin biyu, Shugaban Kotun Cif Ademola Odunade, ya kashe auren da suka shafe shekara 7 suna tare. Kuma ya bayar da umarnin mika ’ya’yansu biyu ga mahaifiyarsu Rukayyat inda za ta rika kula da su har zuwa shekaru 10.

Shugaban Kotun ya umarci Kamarudeen ya rika kawo Naira dubu 20 a kowane wata ga kotun domin mika wa tsohuwar matarsa a matsayin kudin abinci da kula da lafiyar ’ya’yansu da karatunsu.