Kotun sasanta rikicin ma’aikata ta dakatar da kungiyoyin kwadago da mukarrabanta shiga yajin aiki ko hana ma’aikata gudanar da ayyukansu daga ranar Litinin 28 ga Satumba.
Ta umarci kungiyoyin da jami’ansu, wakilansu ko wani duk wani mai hulda da su kar su kuskura su kawo tsaiko ga gudanar da ayyuka ko hana ma’aika da sauran ’yan Najeriya gudanar da harkokinsu a ranar ko wata rana ta daban.
- Yajin aiki: Gwamnoni za su yi zaman gaggawa
- Ambaliya ta ci mutum 5 da rabin gari a Jigawa
- Najeriya ta yi alkawarin damawa da nakasassu
Mai Shari’a Ibrahim Galadima ya ce hakan al’amura za su ci gaba da kasancewa har sai kotun ta yi saurari karar da aka shigar a gabanta.
Wata gamayyar kungiyoyin wanzar da zaman lafiya ce ta shigar da karar tana neman kotun ta hana kungiyoyin kwadago shiga yajin aiki.
Idan ba a manta ba kungiyoyin kwadago sun yi barazanar fara yajin aiki da zanga-zanga a fadin Najeriya domin matsa wa Gwamantin Tarayya lamba ta soke karin farashin man fetur da wutar lantarki da aka yi.