Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Kotu ta haramta wa INEC soke rajistar jam’iyyu 31

Farfesa Yakubu Mahmud

Kotu ta haramta wa INEC soke rajistar jam’iyyu 31

Wata babbar kotu da ke Abuja, ta dakatar da Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC daga soke rijistar jam’iyyu 31.

Kotun ta soke jam’iyyun ne karkashin mai shari’a Anwuli Chikere, inda ta ce hukuncin ya biyo bayan karar da jam’iyyun da aka soke rajistar tasu suka shigar gabanta. Kamar  yadda kamfanin dillanci labarai NAN ya sanar.

A ranar 6 ga Fabrairun 2020 ne Hukumar INEC ta soke rajistar jam’iyyun siyasa 74.

https://aminiya.dailytrust.com.ng/inec-ta-soke-jamiyyun-siyasa-74-daga-cikin-91/

Shugaban Hukumar INEC Farfesa Mahmud Yakubu, ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai, lokacin da aka soke jam’iyyun.

Farfesa Mahmud, ya ce jam’iyyu 16 ne kawai suka cika ka’idojin da tsarin mulkin Najeriya na 1991 (wadanda aka yi wa kwaskwarima) ya tanadar.