Da Dumi Dumi

Kotu ta janye daga tuhumar Ronaldo

Shahararren dan wasan Portugal ba zai fuskanci shari’a bayan da aka zarge shi da yi wa wata fyade a birnin Las Vegas na Amurka, kamar yadda BBC ta kalato.

Kathryn Mayorga ce ta zargi dan kwallon na Juventus da yi mata fyade a wani otal a birnin a 2009.

Rahotanni sun ce ta sasanta da shi a wajen kotu a shekara ta 2010, amma ta so ta sake shigar da kara a 2018.

Ya musanta dukkan zarge-zargen da ta yi masa.

A sanarwar da suka fitar ranar Litinin, masu gabatar da kara a Las Vegas sun ce sun “kasa tabbatar da zarge-zargen”.

ADVERTISEMENT

Ronaldo bai musanta cewa sun hadu a Las Vegas a 2009, sai dai ya ce duk abin da suka yi, sun yi ne da yardar juna.

Ronaldo ya koma Juventus a watan Yulin bara. Ya lashe kyautar dan kwallon da ya fi kowa hazaka a duniya ta Ballon d’Or – a shekarun 2008, 2013, 2014, 2016 da 2017.

Share