Da Dumi Dumi

Kotu ta kori Sanata Dino Melaye ta bayar da umarnin sake zaben

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta kori Sanata mai Wakiltar Kogi ta Yamma Dino Melaye, a jihar Kogi. Kotun ta yanke hukuncin hakan ne bayan sauraron kararrakin zaben ‘yan majalisar tarayya da na jihohi da aka shigar.

Kotun ta ce, ba a gudanar da sahihin zabe ba wajen zabar Sanata Dino Melaye, wanda ke takara na jam’iyyar PDP.

Kotun ta umarci Hukumar zabe ta kasa INEC da a sake gudanar da zaben mukamin Sanata Dino daga yanzu zuwa kwanaki 90.

Share