Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Kotu ta kori shugaban APC na jihar Anambra

Babbar kotun tarayya da ke Awka babban birnin jihar Anambra, ta yi watsi da zaben Mista Emeka Ibe a matsayin shugaban jam’iyyar APC na jihar.

Wanda ya shigar da karar kuma dan takarar neman kujerar shugaban jam’iyyar Cif Uzochukwu Onyekwere, ya bukaci kotun da ta yi binciken zaben da aka yi na ranar 19 ga watan Mayu wanda ya yi sanadiyar kasancewar Ibe a matsayin shugaban jam’iyyar.

ADVERTISEMENT

Bayan kammala binciken kotun ta ce, ba a gudanar da sahihin zabe don haka ta kori shugaban jam’iyyar daga mukaminsa.

ADVERTISEMENT