✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta sake daure Nawaz Sharif shekara 7

Kotu ta sake yanke wa tsohon Firayi Ministan Pakistan Nawaz Sharif hukuncin dauri kan wata sabuwar tuhumar aikata almundahana. Kotun Yaki da Cin hanci da…

Kotu ta sake yanke wa tsohon Firayi Ministan Pakistan Nawaz Sharif hukuncin dauri kan wata sabuwar tuhumar aikata almundahana.

Kotun Yaki da Cin hanci da Rashawa a Islamabad ta daure Sharif din na tsawon shekara bakwai a gidan yari saboda yadda jarinsa ya haura asalin kadarorin da ya mallaka.

Mista Sharif wanda ya sha musanta aikata ba daidai ba, an taba daure shi a watan Yuli kan wata shari’a ta daban, amma aka ba da belinsa bayan wata Babbar Kotu a Islamabad ta dakatar da hukuncin a watan Satumba kamar yadda BBC ya ruwaito.

Nawaz Sharif ya kasance Firayi Ministan Pakistan daga ranar 5 ga watan Yuni 2013 zuwa 28 ga watan Yulin 2017.

Nawaz Sharif ya sauka ne bayan Alkalin Kotun Kolin Pakistan ya sauke shi daga mukaminsa.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan wani bincike da aka yi kan dukiyar iyalinsa sakamakon abin fallasar nan na Panama Papers, wanda ya gano cewa yana da dukiya a kasashen da ke kauce wa biyan haraji.

Bayan yanke masa sabon hukuncin, jam’iyyarsa ta Muslim League-Nawaz ta yi barazanar kaddamar da zanga-zanga tare da dagula lamurran majalisa idan har aka sake tura shugabanta gidan yari.

Haka kuma jami’an tsaro sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa magoya bayansa a harabar kotun.

Sharif ya ce siyasa ce kawai a shari’ar da ake masa, inda ake sa ran zai daukaka kara.