✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta sake mallaka wa gwamnati Naira biliyan 7.6 na Diezani

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta mallaka wa Gwamnatin Tarayya Naira biliyan 7 da miliyan 600 da ake zargin tsohuwar Ministar Mai Misis…

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta mallaka wa Gwamnatin Tarayya Naira biliyan 7 da miliyan 600 da ake zargin tsohuwar Ministar Mai Misis Diezani Alison-Madueke da sacewa.

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) ce ta gano kudin a wani banki, inda ta yi zargin cewa tsohuwar Ministar ta same su ne ta hanyar da ba ta dace ba. Kuma EFCC ta ce an ajiye kudin ne a asusu daban-daban.

Alkalin Kotun Mai shari’a Abdulaziz Anka ya yanke hukuncin ne bayan da Hukumar EFCC ta nemi kotun ta mallaka wa gwamnati kudin dindindin.

A farkon watan Agusta ma wata Babbar Kotun da ke Legas ta mallaka wa gwamnatin wasu kadarorin tsohuwar Ministar da suka kai Dala miliyan 40, wato kimanin Naira biliyan 14.

Kotun ta kuma mallaka wa Najeriya wani katafaren gidan Misis Diezani da ke yankin Banana Island a Legas, wanda kudinsa ya kai Dala miliyan 37.5, kimanin Naira biliyan 13.

Mai shari’a Chuba Obiozor ya mallaka wa gwamnatin sama da naira miliyan 84 da rabi da kuma sama da Dala miliyan biyu, wasu kudaden da aka karba a matsayin na haya na gidan na Banana Island.

A kwanan baya dai kotun ta bai wa gwamnatin kasar damar kwace kadarorin na wucin-gadi, bayan Hukumar EFCC ta bukaci kotun ta mallaka wa gwamnati kadarorin.

Bayan haka ne kotun ta ba da umarnin a buga hukuncin a gidajen jaridu, domin duk wanda ke da wani dalilin da zai sa ba za a mallaka wa gwamnati kadarorin na dindindin ba ya kawo dalilinsa a gaban kotun.

A watan Afrilun bara, Hukumar EFCC ta kwace gwala-gwalan da darajarsu ta kai ta Naira miliyan 593 daga hannun tsohuwar Ministar.

Ana zargin Diezani da sacewa da kuma yin facaka da kudin kasar nan a lokacin da take Ministar Mai, sai dai ta sha musanta zargin.

A watan Fabrairun bana ma, wata Babbar Kotun Tarayya ta amince a halatta tare da mallaka wa gwamnati  kudaden da aka samu a wajen Diezani Allison-Madueke.