✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta samu Oliseh Metuh da laifin karbar Naira miliyan 400

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta samu tsohon kakakin jam’iyyar PDP Olisa Metuh, da laifin karbar Naira miliyan 400 daga hannun tsohon Mashawarcin…

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta samu tsohon kakakin jam’iyyar PDP Olisa Metuh, da laifin karbar Naira miliyan 400 daga hannun tsohon Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro Sambo Dasuki.

Mai shari’a Okon Abang, ne ya sanar da hakan ranar Talata, saboda Olisa Metuh ya gaza gamsar da kotun cewa, kudaden da ake zarginsa an ware su ne don zaben shekarar 2015 na tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan.

Okon, ya kara da cewa Olise Metuh bai gamsar da kotun cewa, baida wata masaniya game da tusa masa kudaden daga ofishin Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro zuwa asusun bakinsa ba da kamfaninsa mai suna Destra Investment Ltd. A shekarar 2016 an samu Olise Metuh da almundahanan kudade bayan Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta gurfanar da shi.