✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta soke sababbin sarakunan Kano

Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta soke sababbin sarakuna hudu da Gwamnatin Jihar ta kirkiro a matsayin masu daraja ta daya wata shida baya. Mai…

Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta soke sababbin sarakuna hudu da Gwamnatin Jihar ta kirkiro a matsayin masu daraja ta daya wata shida baya.

Mai shari’a Usman Na’abba ne ya yanke hukuncin, inda ya ce kirkiro sababbin masarautun hudu ya saba ka’ida.

Idan ba a manta ba, a ranar 8 ga Mayu ne Gwamnan Jihar Kano Dokat Abdullahi Umar Ganduje ya rattaba hannu a kan dokar da ta kirkiro sababbin masarautun hudu masu daraja ta daya.

Masarautun su ne, Bichi da Rano da Gaya da Karaye.

Da yake yanke hukuncin a jiya Alhamis, Mai shari’a Na’abba ya ce Majalisar Dokokin Jihar Kano ta saba ka’ida da dokar sashe na 101 na kundin tsarin mulkin kasa na 1999, wanda ya ba majalisar damar yin doka.

Wanda hakan ya sa kotun ta yi watsi da kirkiro sababbin masarautun. Da wannan hukunci bangaren da bai yarda ba zai iya zuwa kotun gaba har zuwa Kotun Koli.