Search
Subscribe
Kotu ta soke zaben Doguwa da Jibrin Kofa

Alhaji Alhassan Ado Doguwa

Kotu ta soke zaben Doguwa da Jibrin Kofa

Kotun Daukaka Kara da ke  Kaduna ta soke zaben dan Majalisar Bebeji da Kiru Alhaji Jibirin Kofa da kuma Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai kuma mai wakilatar Doguwa daTudun Wada da ke Jihar Kano, Alhaji Alhassan Ado Doguwa. Za a sake zabe a wasu mazabu na mazabar Bebeji Kiru, yayin da ta bayyana soke dukkan zabubbukan da aka yi a kananan hukumomi biyu na Doguwa da Tudun Wada bisa hujjar an cire sunayen sauran jam’iyyu a lokacin zaben.

Alkalin Kotun Oludotun Adefope-Okojie, ya yanke hukuncin a sake zabe a kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada.

Kotun ta ce zaben bai inganta ba kasancewar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ba ta bai wa wasu jam’iyyu dama ba a lokacin bayyana sakamakon zaben.

Kotun ta bai wa Hukumar INEC  kwana 90 domin ta sake gudanar da zabe a kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada da Kiru da Bebeji.

Kotun Sauraron Kararrakin Zabe ta yi watsi da karar da Yusha’u Salisu na Jam’iyyar PDP ya shigar, bisa gaza gamsar da kotun kan zarge-zargen magudi. To sai dai Kotun Daukaka Karar ta ce ta yi mamakin yadda kotun zaben ta yi watsi da shaidun da Jam’iyyar PDP ta gabatar mata.

Wannan dai na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da wata kotun daukaka kara ta soke zaben dan majalisar Kiru/Bebeji, Abdulmuminu Jibril.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin