Da Dumi Dumi

Kotu ta soke zaben Sanatan APC ta bai wa ’Yar takarar PDP

Kotun Daukaka kara da ke Kaduna ta soke zaben Dan Majalisar Dattawa Sanata Dayo Adeyeye kuma Kakakin Majalisar Dattawan na jam’iyyar APC, daga mazabar jihar Ekiti ta Kudu.

Kotun ta yanke wannan hukuncin ne bayan ‘yar takarar Sanata ta PDP Biodun Olujimi, ta shigar da karar kan kalubalantar nasarar zaben Sanata Dayo Adeyeye da aka yi ranar 23 ga Fabrairu 2019.

Bayan sauraran kararrakin zaben da aka yi yau Laraba kotun ta tabbatar ‘yar takarar PDP Sanata Biodun Olujimi, a matsayin wanda ta lashe zaben kujerar Sanatar mazabar Ekiti ta Kudu.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya