✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tabbatar da zaben gwamnonin Bauchi da Benuwai

Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamna ta tabbatar da zaben da aka yi wa Sanata Bala Muhammad Abdulkadir a matsayin Gwamnan Jihar Bauchi. Da yake karanto…

Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamna ta tabbatar da zaben da aka yi wa Sanata Bala Muhammad Abdulkadir a matsayin Gwamnan Jihar Bauchi.

Da yake karanto hukuncin kotun a madadin sauran alkalai biyu, Shugaban Kotun, Mai shari’a Salihu Shu’aibu ya ce, karar da tsohon Gwamnan Jihar, Mohammed Abdullahi Abubakar ya kai kan zaben Sanata Bala Mohammed kara ce da ba ta da inganci saboda  zaben na bana sahihin zabe ne mai cike da gaskiya.

Mai shari’a Shu’aibu ya kori karar bisa cewa masu kara sun gaza tabbatar da zargin magudin zabe. Kuma zargin da suke yi bai tabbata ba saboda shaidun da suka gabatar sun gaza tabbatar da ikirarinsu na aikata ba daidai ba lokacin zaben.

Shugaban kotun wanda ya shafe sa’o’i shida da rabi yana karanto hukuncin, ya bi bahasin shari’ar da bayanan da shaidun masu kara daya bayan daya inda ya ce dukkan shaidun sun gaza tabbatar da wani magudi ko al’mundahana ko rashin bin ka’ida a lokacin gudanar da zaben.

Sai alkalin ya tabbatar da zaben Sanata Bala Mohammed Abdulkadir a matsayin Gwamnan Jihar Bauchi.

Lauyan PDP Chris Uche ya ce gaskiya ta yi halinta ya kuma gode wa kotun saboda tsage gaskiya da ta yi.

Sakataren Jam’iyyar APC ta Jihar Bauchi, Hussaini Bako ya ce wannan shari’a ta farko ce, kuma za su zauna da sashensu na shari’a su nazarci hukuncin don sanin matakin da za su dauka. Ya roki magoya bayansu su kara hakuri su saurari shawarar da masana shari’ar za su ba su.

Babban Lauyan tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abubakar da Jam’iyyar APC a shari’ar zaben  Gwamnan Jihar, Ishiaku Dikko ya ce za su duba hukuncin da kotun ta yanke, sannan su san matakin da za su dauka a gaba.

Ishiaku Dikko (SAN) wanda ya shigar da kara a madadin Jam’iyyar APC da tsohon Gwamnan ya fada wa manema labarai cewa akwai bukatar su duba hukuncin da aka yi, su kuma tattauna kafin daukar mataki a kai.

Gwamna Bala Mohammed, ya yi sujudar godiya ga Allah, jim kadan da yanke hukuncin, wanda ya bayyana shi da nasarar al’ummar Jihar Bauchi.

Daga bisani Gwamnan ya fito kan mota inda aka yi gangami daga gidan gwamnati zuwa ofishin Jam’iyyar PDP na jihar.

A Jihar Benuwai ma kotu ta tabbatar da zaben Gwamna Samuel Ortom wanda dan takarar Jam’iyyar APC, Emmanuel Jime ya kai shi kotun yana kalubalantar nasararsa a zaben na 9 ga Maris.

Dan takarar APC  ya kalubalanci sakamakon zaben kananan hukumomin 11 inda ya ce an tafka magudi a cikinsu lokacin zaben.