Search
Subscribe
Kotu ta tabbatar da zaben Sanata Suswam

Sanata Gabriel Suswam

Kotu ta tabbatar da zaben Sanata Suswam

Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamna da na Majalisar Dokoki da ke zama a Makurdi, babban birnin Jihar Benuwai, ta tabbatar da nasarar da  tsohon Gwamnan Jihar Mista Gabriel Suswam ya samu a  zaben Sanata mai wakiltar Benuwai ta Arewa maso Gabas. Kotun mai alkalai uku a karkashin jagorancin Mai shari’a A. O. Odugu a ranar Talatar da ta gabata, ta yi watsi da karar da dan takarar Jam’iyyar APC,  Mista Mimi Orubibi ya shigar inda yake kalubalantar nasarar da tsohon Gwamnan ya samu, a zaben da aka gudanar ranar 23 ga Farairu kamar yadda Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito.

Kotun ta kori karar ce aan hujjar cewa mai karar ya gaza tabbatar da zarginsa na cewa an yi magudi yayin gudanar da zaben kamar sayen kuri’u da sauran laifuffukan karya doka. Don haka ta bukaci mai karar ya biya Naira dubu dubu 100 ga  Sanata Suswam na Jam’iyyar PDP. Da suke tofa albarkacin bakinsu a kan hukuncin kotun, lauyoyin Sanata Suswam, Andrew Womo, da na Orubibi Frank Noomor, sun ja layi a kan fassarar sashi 138 na dokar zabe da kuma bukatar yin gwaji kan sakamakon hukuncin a Kotun Daukaka Kara.

A wani lamarin kuma a ranar Talatar ce Kotun Koli ta kwace kujerar dan Majalisar Jihar Ondo mai wakiltar mazabar Okitipupa  ta Biyu, Mista Sina Akinwumi, wanda dan Jam’iyyar APC ne. Dama Babbar Kotun Jihar Ondo da Kotun Daukaka Kara da ke Akure suka soke zaben fid da gwani da ya kai dan majalisar kujerarsa a zaben da aka gudanar ranar 9 ga watan Maris, inda suka yanke hukuncin cewa James Ololade-Gbegudu ke da kujerar.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin