✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tabbatar wa Matawalle kujerarsa

Kotun Sauraron Kararrakin Zaben  Gwamnan Jihar Zamfara da ke zama a Abuja, ta yi watsi da karar da ke bukatar sauke Gwamna Bello Matawalle daga…

Kotun Sauraron Kararrakin Zaben  Gwamnan Jihar Zamfara da ke zama a Abuja, ta yi watsi da karar da ke bukatar sauke Gwamna Bello Matawalle daga kujerarsa. Karar da Muhammed Takori na Jam’iyyar APDA ya shigar a kan Matawalle da Hukumar INEC an yi watsi da ita.

Takori da Jam’iyyar APDA sun shigar da karar ce don bukatar a sauke Matawalle daga kujerar Gwamnan Jihar saboda bai ci kuri’u biyu bisa uku na jimillar kuri’un jihar kamar yadda doka ta tanadar.

Amma yayin yanke hukuncin, kotun a karkashin jagorancin Mai shari’a Binta Zubair, ta yanke hukuncin cewa karar ba ta da makama kamar yadda Kotun Koli ta bayyana tun a ranar 24 ga Mayun bana. Mai shari’a Zubair ta kara da cewa, kuri’un da PDP ta samu a zaben 9 ga Maris a Jihar Zamfara su ne halatattun kuri’u a zaben Gwamnan.

Tun farko kotun zaben ta yi watsi da ikirarin Takori da ya ce PDP ba ta yi zaben fid-da-gwani ba kuma jam’iyyar ba ta dauki nauyin Matawalle ba, don haka bai dace da takarar Gwamnan Jihar Zamfara ba.

Mai shari’ar ta yank ewa masu karar tarar Naira dubu 500 da za su biya Gwamna Matawalle.

Idan za a tuna, Hukumar zabe INEC ta bayyana Mukhtar Idris na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Jihar Zamfara, a zaben 9 ga Maris da aka yi. Amma sakamakon rashin yin zaben fid-da-gwani kamar yadda doka ta tanada, sai Kotun Koli ta kwace kujerar ta mika wa Bello Matawalle na Jam’iyyar PDP wanda ya zo na biyu a lokacin zaben a matsayin wanda ya lashe zaben.