✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare budurwar da ta zargi saurayinta da yi mata ciki

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Karamar Hukumar Taura a Jihar Jigawa ta tura wata budurwa gidan yari na tsawon mako uku bayan da ta…

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Karamar Hukumar Taura a Jihar Jigawa ta tura wata budurwa gidan yari na tsawon mako uku bayan da ta yi karar saurayinta tana neman kotun ta bi mata hakkinta saboda a cewar budurwar saurayin nata ya yi mata ciki sannan ya yi watsi da ita, ya kuma karya alkawarin da ya yi mata cewar zai aure ta.

Yarinyar mai suna Ummi Magaji Kwalam ta shigar da karar ce a gaban kotun amma sai reshe ya juye da mujiya, inda maimakon a daure saurayin nata mai suna Sadam Aliyu Kwalam wanda ta yi zargin ya yi mata ciki, sai kotun ta tsare ta.

Da yake mayar da jawabi, Kakakin Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa, Malam Auwalu Sani Balago ya ce hukuncin da wancan alkali ya yi ya saba wa ka’ida, ba a yi hukuncin bisa doron shari’a ba, kamata ya yi a ce idan za a yi wa yarinyar hukunci a tura su gidan yarin tare kuma a yi musu horo iri daya, domin dukansu masu laifi ne.

“Amma ba ya cikin ka’ida a tsare wanda ya yi kara a saki wanda ake kara domin wadna ake kara ya zagaya ya diro ta sama ya yi amfani da ’yan sanda sun gabatar da korafinsa a gaban kotu, alhali yana da laifi,” inji shi. Ya ce sun bincika sun gano shi wanda ake karar ne ya zagaya ya yi riga malam masallaci ya yi karar yarinyar a wajan ’yan sanda su kuma suka gabatar da kararsa a gaban kotun.

Ya kara da cewa Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Jigawa ta umarci alkalin da ya tura a dauko yarinyar daga gidan yari kuma a ba da ita beli, kuma a tura wa wancan saurayi takardar gayyata a gaban kotu domin a yi nazari a kan shari’ar saboda a bai wa kowa hakkinsa.

Da yake amsa tambayoyin wakilinmu, mahaifin yarinyar mai suna Malam Magaji Tela Kwalam ya ce kowa ya sani kaf cikin danginsu Sadam ne ya yi wa ’yarsa Ummi ciki kuma shi ne yake daukarta yake tafiya daji da ita har ya yi mata ciki.

Saboda an ga su marasa karfi ne shi ne ya sa wasu suka gwada wa yaron dabara ya riga suzuwa  wajen ’yan sanda ya shigar da kara kafin yarinyar ta gabatar da kara a kotu, shi ne ’yan sanda suka kama ’yarsa suka gabatar da ita a gaban kotu wai tana son ta bata wa dansu suna.

“Saboda haka aka bukaci Ummi ta gabatar da shaida a gaban alkali cewa Sadam ne ya yi mata ciki, saboda Ummi ba ta fadi wasu shaidu ba, alkali ya sa ’yan sanda suka ingiza keyarta zuwa gidan yari da ke Gumel na tsawon mako uku zuwa lokacin da kotun za ta yi nazari a kan shari’ar domin yi mata hukunci,” inji mahaifin nata.

A lokacin da wakilimmu ya tuntubi Alkalin Kotun, Mai shari’a Aliyu Muhammed ta wayar salula ya ce ba zai yi magana da manema labarai ba a kan wannan shari’a sai dai a tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Sharia ta Jihar Jigawa.