✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare likita kan zubar da ciki ga karamar yarinya

Babbar Kotun Majistare ta Biyu da ke garin Kafanchan ta tsare wani likita mai suna Dokta Joe Orukwe da wani mutum  mai suna Godwin Ikechukwu…

Babbar Kotun Majistare ta Biyu da ke garin Kafanchan ta tsare wani likita mai suna Dokta Joe Orukwe da wani mutum  mai suna Godwin Ikechukwu a gidan yari na Kafanchan bisa  zarginsu da laifin hada baki wajen  sanadiyyar mutuwar jariri ta hanyar zubar da ciki.

Dokta Orukwe, wanda aka dade da zarginsa da zubar da ciki musamman ga kananan yara shi ne mamallakin Asibitin Bethel da ke Layin Gurara a garin Kafanchan.

Likitan ya shiga hannu ne bayan zargin zubar da cikin wata yarinya ’yar shekara 14 da aka sakaya sunanta, wadda ake zargin dan uwan mahaifinta Godwin Ikechukwu da lalata da ita har ta kai ta ga daukar ciki kuma ya dauke ta zuwa Asibitin Bethel tare da hada baki da likitan inda suka zubar da cikin.

Yayin da take yi wa Aminiya karin bayani, Shugabar Cibiyar Sauraron Koke-Koke Kan Laifuffukan Cin Zarafin Mata da Kananan Yara ta Salama da ke Babban Asibitin garin Kafanchan, Misis Grace Yohanna Abbin ta ce sun samu rahoton abin da Ikechukwu ya aikata ne ta hanyar mahaifin yarinyar, bayan tun farko wani makwabcinsu ya fara tsegunta musu, inda cibiyar tare da hadin gwiwar abokan aikinta jami’an tsaro na NSCDC, Shiyyar Kafanchan suka yi nasarar kamo shi bayan likitan cibiyar mai suna Dokta Bakwot Gilbert ya tabbatar da zubar da cikin ta hanyar gwaje-gwaje.

Ta ce ba wannan ne karo na farko da ake zargin likitan da zubar wa kananan yara mata ciki ba. “Akwai lokacin da aka taba tsare shi bayan an bayar da belinsa da nufin kai shi kotu kafin ranar zuwa kotun sai da ya sake zubarwa wa wata karamar yarinya ciki amma ya gudu bayan ya samu labarin asirinsa ya tonu,” inji ta.

Ta ce tun watan Nuwamban bara ya gudu sai a bana suka yi nasarar kama shi tare da wanda ya ake zargi da yi wa yarinyar ciki kuma ya kai ta aka zubar sannan suka mika su ga kotu don yin hukuncin da ya dace inda ta tsare su a gidan yari.

Misis Abbin ta bayyana takaicinta kan yadda har yanzu mutane ke cin zarafin kananan yara ta hanyar bata musu rayuwa tun suna kanana da kuma kananan yaran da kan yi watsi da damarsu ta hanyar rungumar hanyar da ba za ta bulle da su ba duk da irin matakan wayar da kai da cibiyarsu ke gudanarwa a makarantu da sauran cibiyoyi.