Da Dumi Dumi

Kotu ta tura malaman Islamiyya 6 gidan yari a Kaduna 

Wata kotu da ke a Kaduna ta tura malaman makarantar Imam Ahmad Bn Hambal da ke Rigasa gidan yari a yau Litinin. 

Rundunar ‘yan sandan jihar ne ta gabatar da malaman a gaban mai shari’ar Musa Mohammed Auwal a Kotun Majistare da ke zama a titin Ibrahim Taiwo jihar Kaduna.

An kuma kaisu kotun ne da misalin karfe 1 na rana, sannan aka soma zaman saurarar karar da misalin karfe 2 na rana kuma aka kammala zaman kotun da misalin karfe 3:30 na yamma.‎

Wadanda aka gabatar a gaban kotun su ne: Ismail Abubakar da Umar Abubakar da Abdul’azeez Adam da Abubakar Muktar da Abdullahi Auwal sai kuma Salisu Ibrahim.‎

Dan Sanda mai gabatar da kara Hassan M. Malan, ya bayyanawa kotu cewa ana zargin malaman ne da laifin hada baki a aikata laifi da kuma kebe mutane ba bisa ka’ida ba da kuma zargin luwadi.

ADVERTISEMENT

Sai dai Lauya mai kare malaman Shehu Sani Surajo, ya bayyanawa kotun cewa, bata da hurumin saurarar karar dan haka sai ya ce, wadanda ake tuhuma an dai kawo su ne kawai domin bayyana kansu.

Ya kuma bukaci kotu da ta mayar da wadanda ake zargin hannun ’yan sanda har sai an kammala bincike sai dai dan sanda mai gabatar da karar ya ki amincewa da hakan domin a cewarsa ’yan Sanda basu da inda za su a jiye su.

Da yake yanke hukunci mai Shari’a Musa Mohammed Lawal, ya ce hakika kotun bata da hurumin saurarar karar saboda daya daga cikin laifin da ake zarginsu da shi babban laifi ne da sai babban kotu da ke jihar ne ke da hurumin saurara.

Dan haka sai ya ce, a tura da wadanda ake zargin gidan yari har zuwa ranar 29 ga watan nan da muke ciki domin ci gaba da saurarar karar.

Lauyan wadanda ake kara Shehu Sani Surajo, ya bayyanawa manema labarai a wajen kotun cewa, za su nemi belin malaman a babban kotun jihar.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya