✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta umarci Gwamnatin Kano ta mayar da ma’aikatan lafiya bakin aikinsu

Kotun Sasanta Rikicin Ma’aikata ta Tarayya da ke Kano ta umarci gwamnatin jihar ta biya ma’aikatan da ke aiki karkashin Hukumar Kula da Asibitoci ta…

Kotun Sasanta Rikicin Ma’aikata ta Tarayya da ke Kano ta umarci gwamnatin jihar ta biya ma’aikatan da ke aiki karkashin Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar albashinsu tare da mayar da su wuraren ayyukansu na baya.

Ma’aikatan ne suka kai kara kotun suna neman kotun ta agaza musu game da wata takarda da ofishin Shugaban Ma’aikta na Jihar ya fitar a ranar 6 ga watan Satumba 2016 da take bayar da umarnin dauke su daga wuraren aikinsu zuwa wasu ma’aikatu na jihar tare da canja musu tsarin albashinsu daga na ma’aikatan lafiya (CONHESS) zuwa na sauaran ma’aikatan jihar (HAPSS).

Lauyan masu kara Barista Suraj Sabo Ali ya shaida wa kotun cewa kasancewar Hukumar Kula da Asibitoci ta jihar ce ta dauke su aiki suna da hakkin samun albashin ma’aikatan lafiya, haka kuma Ofishin Shugaban Ma’aikata ba ya da hurumin ba su wata takarda,” inji lauyan.

Da yake yanke hukunci, Alkalin Kotun Mai shari’a E.B.E. Isiele ya ce dole ne wanda ake kara ya biya dukanin kudaden da aka rage daga albashin ma’aikatan na tsawon shekara biyu da sauran wasu hakkokinsu wadanda suka rasa sakamakon amfani da waccan takarda ta ofishin Shugaban Ma’aikata.

A nasa bangaren Lauyan kariya, Barista Mukhtar Sani Daneji ya ce za su yi nazari a kan hukuncin don gano ko akwai yiyuwar daukaka kara ko babu.