✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yi fatali da karar da aka shigar kan Obaskeki

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi fatali da karar zargin Gwamnan Edo, Godwin Obaseki da amfani da takardar shaidar karatu ta…

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi fatali da karar zargin Gwamnan Edo, Godwin Obaseki da amfani da takardar shaidar karatu ta bogi.

Mai Shari’a Anwuli Chiekere ya yi watsi da karar a zaman kotun na ranar Litinin 28 ga watan Yuni bayan masu karar sun janye ta bakin lauyansu Kingsley Idahosa.

Da farko masu shigar da karar da suka hada da Edobor Williams, Ugbesia Abudu Godwin da Amedu Dauda Anakhu, na bukatar kotun ta hana Obaseki takarar zaben gwamnan Edo da ke tafe a watan Satumba.

Suna kafa hujja cewa amfani da jabun takardar shaidar kammala karatun digiri da Obaseki ya yi ikirarin samu daga Jami’ar Ibadan, ya saba da sashe na 182, karamin sashe na biyu (i) na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Sai dai Lauyansa Alex Ejesieme (SAN) ya ce zargin ba shi da tushe balle makama.

Tuni dai Gwamna Obaseki ya sami nasarar zama dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP bayan ya lashe zaben fitar da gwani na jam’iyyar kuma zai fafata da Osagie Ize-Iyamu na jam’iyyar APC da sauran ‘yan takara a zaben da ke tafe.