✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yi watsi da bukatar daukaka karar Atiku da PDP

Kotun sauraren karar zaben shugaban Najeriya wanda jam’iyyar adawa ta PDP da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Atiku Abubakar, suka shigar ta yi watsi…

Kotun sauraren karar zaben shugaban Najeriya wanda jam’iyyar adawa ta PDP da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Atiku Abubakar, suka shigar ta yi watsi da daukaka karar na ranar 11 ga watan Yuni 2019 don ci gaba da sauraran karar da ake ciki.

Kotun ta ce, mambobin mutum biyar da suka shigar da bukatar daukaka karar basu da cikakken ‘yancin ci gaba da daukaka karar.

Atiku da jam’iyyar PDP tare da Lauyan da ya jagoranci bukatar daukaka karar Levy Uzoukwu (SAN), sun bukaci kotun da ta soke duk rahotannin da ta tattara tunda ba a basu damar kare kansu akan abin da jam’iyyar APC ta gabatar wa kotun ba.