✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yi watsi da karar dan takarar PDP a zaben Gwamnan Nasarawa

Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Gwamnnan Jihar Nasarawa da ke Lafiya, tayi watsi da karar da dan takarar Gwamnan Jihar a Jam’iyyar PDP ,Honorabul Dabid Ombugadu…

Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Gwamnnan Jihar Nasarawa da ke Lafiya, tayi watsi da karar da dan takarar Gwamnan Jihar a Jam’iyyar PDP ,Honorabul Dabid Ombugadu ya shigar yana kalubalantar nasarar da Gwamnan Jihar Injiniya Abdullahi Sule na Jam’iyyar APC ya samu a zaben bana.

Da yake yanke hukunci a yayin zaman da aka dauki sama da awa 7 ana yi. Shugaban Kotun Mai shari’a Abba Mohammed ya bayyana cewa korafin da Jam’iyyar PDP da dan takararta Dabid Ombugadu suka gabatar a takadar kararsu ba ta da tushe balle makama.

A cewarsa wanda ya shigar da  karar ya kasa gabatar wa kotun hujjojin da za su gamsar da kotun cewa lallai an yi aringizon kuri’u a yayin zaben, sannan an kuma tafka kura-kurai a wajen gudanar da zaben da suka saba ka’idodin hukumar zabe da sauransu kamar yadda suka yi korafi. Ya kara da cewa wanda ya shigar da karar ya kuma kasa gabatar da hujjojin da za su tabbatar da an dakatar da zabubbuka a wasu mazabu.

A dalilin rashin gabatar da sahihan shaidu da kuma kwararan hujjoji ya sa kotun ta yi watsi da karar inda ta tabbatar da nasarar Gwamna Abdullahi Sule na Jam’iyyar APC a matsayin zababben Gwamnan Jihar a zaben bana kamar yadda doka ta tanada. Ya ci gaba da cewa “Tunda wanda ya shigar da karar ya kasa gabatar da wadannan hujjoji tare da wasu da dama ya zame wa kotun dole ta tabbatar tare da amincewa da sakamakon zabubbukan da hukumar zabe ta kasa ta bayyana. Idan za a iya tunawa jim kadan da bayyana sakamakon zaben Gwamnan Jihar wanda aka bayyana Injiniya Abdullahi Sule ne ya yi nasara, sai dan takarar Jam’iyyar PDP  wanda tsohon dan majalisar wakilai ta tarayya ce Honorabul Dabid Ombugadu ya shigar da kara a kotun inda ya kalubalanci nasarar da Abdullahi Sule ya samu.

Gwamna Abdullahi Sule ya lashe zaben ne da kuri’a dubu 327 da 229 yayin da Ombugadu ya samu kuri’a dubu 184 da 281 kamar yadda hukumar zabe ta bayyana sakamakon a lokacin.