✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Afirka ta Kudu ta ce a kama Jacob Zuma

Wata kotu a Afirka ta Kudu, ta ba da waranti a kama tsohon Shugaban Kasar Mista Jacob Zuma, saboda ya ki bayyana a gaban kotu…

Wata kotu a Afirka ta Kudu, ta ba da waranti a kama tsohon Shugaban Kasar Mista Jacob Zuma, saboda ya ki bayyana a gaban kotu a ranar Talatar da ta gabata a zaman shari’ar da ake tuhumarsa da wasu laifuffuka.

Ana zargin Mista Zuma ne da karbar cin hanci daga wani kamfanin Faransa mai kera makamai da ake kira Thales, wanda ya rattaba hannu kan kwantaragin Dala biliyan biyu da kasar.

Lamarin ya faru ne a 1999  lokacin Zuma na matsayin Mataimakin Shugaban Kasar.

Ana tuhumar Zuma da laifuffuka 16 da suka hada da damfara da zamba cikin aminci.

Sai dai lauyoyin Zuma, sun gabatar da wata wasika da wani likitan sojoji ya sa wa hannu, wacce ta nuna cewa tsohon Shugaban ba ya da lafiya, ya kuma fita kasar waje ganin likitoci, wasikar da alkalin ya nuna shakku a kanta.

Sai dai alkalin, ya jingine warantin kama Zuma zuwa ranar 9 ga Mayu, lokacin da za a sake zaman sauraren karar.