✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun CCT ta umurci a kama Onnoghen

Kotun Da’ar Ma’aikata (CCT) ta bayar da umarni ga Sufeto Janar da Hukumar Tsaron Kasa (DSS) su kamo mata Babban Jojin Najeriya da aka dakatar,…

Kotun Da’ar Ma’aikata (CCT) ta bayar da umarni ga Sufeto Janar da Hukumar Tsaron Kasa (DSS) su kamo mata Babban Jojin Najeriya da aka dakatar, Mai shari’a Walter Onneghen. Umarnin hakan ya fito daga kotun ne a shekaranjiya Laraba lokacin da Shugaban Kotun,  Mai shari’a Danladi Umar ya umarci Sufeto Janar na ’Yan sanda da sauran jami’an tsaron kasar nan su kamo Onneghen su gurfanar da shi a gaban kotun bisa tuhumarsa da laifin kin bayyana kadarorin da ya mallaka.

Mai shari’a Umar ya ce, babu yadda za a yi saurari musanta tuhumar wanda ake tuhuma ba tare da kotu ta ji bahasinsa ba.

“La’akari da wannan hujja ta sama kuma la’akari da cewa kotun ta ba wanda ake tuhuma damar ya bayyana gabanta a lokuta da dama kuma ya gaza bayyana, don haka kotun nan ta mika warantin kamo wanda ake tuhuma ga Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro don su gurfanar da shi a gaban kotun yau Jumu’a  donn sauraren shari’arsa.