✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da zaben Uba Sani

Kotun Daukaka Kara ta Tarayya da ke Kaduna ta tabbatar da zabe Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Uba Sani. Da yake zartar da…

Kotun Daukaka Kara ta Tarayya da ke Kaduna ta tabbatar da zabe Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Uba Sani. Da yake zartar da hukunci a kan karar da Lawal Adamu na Jam’iyyar PDP ya shigar, alkalin kotun Mai shari’a A.O. Okojie ya yi watsi da karar kan rashin hujja mai karfi, don  haka ya tabbatar wa Sanata Uba Sani na Jam’iyyar APC kujerarsa a matsayin wanda ya yi nasara.

Da yake jawabi ga manema labarai kan hukuncin, daya daga cikin lauyoyin Uba Sani, Frank Ikpe (SAN) ya bayyana hukunci a matsayin mai cike da adalci kuma ya ce ya yi daidai da tsarin doka. A cewarsa hukuncin Kotun Daukaka Karar ya tabbatar da hukuncin Kotun Sauraren Kararrakin Zabe, ya ce hakika alkalan sun tabbatar da hukuncin a kan lamura uku da suka hada da ko Uba Sani ya cancanci yin takara, walau na mukamin gwamnati ko rike mukamin siyasa.

Ya kara da cewa kotun zaben ta tababbatar da cewa takardun da dan takarar PDP, Lawal Adamu, ya gabatar ba sa bisa doka.

Shi ma wani lauyan Sanata Uba Sai, Barista Suleiman Shu’aibu ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ce ga dimukaradiyya.