Da Dumi Dumi

Kotun Koli: An dage gabatar da shara’ar jihohin Bauchi da Filato

Gwamna Jihar Bauchi Bala Mohammed
Gwamna Jihar Bauchi Bala Mohammed
A ci gaba da gabatar da shari’un zabe, Kotun Kolin ta dage ci gaba da gabatar da shari’un jihohin Bauchi da Filato zuwa karfe 3 na rana.

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulakadir Muhammed ya zo kotun da safiyar yau tare da rakiyar mukarrabansa, inda yake neman kotun ta tabbatar da zabensa a matsayin Gwamnan Jihar Bauchi.

Idan ba a manta ba, Gwamna Bala ya doke tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Barista MA Abubakar na Jam’iyyar APC ne a zaben 9 ga watan Maris na bara.

Share