Da Dumi Dumi

Kotun Koli: Shugaba Buhari ya taya Ganduje, Lalong murna

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aika da sakon taya murna ga Jam’iyyar APC bisa nazarar da suka samu bayan tabbatar da zabukan Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da takwaransa na Filato, Simon Lalong.

A wata sanarwa da mataimakinsa na musamman kan harkokin watsa labarai Garbe Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya ce, “ina murna maganar ta zo karshe, kuma jam’iyyarmu ce ke da nasara da kuma gwamnoninmu. APC ta lashe zabukan jihohin, kuma kotu ta tabbatar da haka. Da ya kasance abin damuwa idan aka ce jihohin masu muhimmanci kamar Kano da Filato kotu ta kwace su.”

A daidai lokacin da gwamnonin APC din suke murna samun nasarar zabe, Shugaba Buhari ya hori ’yan siyasa da masu zabe su dage wajen tabbatar an gyara dimokuradiyyar kasar wajen nemo hakkinsu a kotu.

Share