Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Kotun koli ta bawa jam’yyar PDP kujerar dan majalisar tarayya na APC, a jihar Adamawa

PDP vs APC

A ranar Talatar da ta gabata ne Kotun Koli ta karbe kujerar dan Majalisar Tarayya na jami’yyar APC Aliyu Modibbo da ke wakiltar mazabar Yola ta kudu da ta Arewa da kuma Girei, tun farko dai Kotun daukaka kara a Yola ce ta halasta zaben Modibbo a karkashin jam’iyyar APC.

Sai dai kuma Kotun Koli ta yi watsi da hukuncin na Kotun daukaka karar ta Yola. Ta kuma amince da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke na cewar dan takarar PDP ne ke da nasara.

ADVERTISEMENT

Kotun Koli ta ki amincewa da hukuncin da Kotun daukaka karar ta yanke, wadda ta mika nasarar ga wani dan takara daban na APC mai suna Mustapha Usman.

Tun da farko a Babbar Kotun Yola, wanda ya shigar da karar ya yi korafin cewa Modibbo na APC wanda aka bai wa Nasara bai cancanci ya tsaya takarar shiga zabe ba, domin bai kammala aikin yi wa kasa hidima ba, (NYSC).

ADVERTISEMENT

Mai shigar da karar ya ce har zuwa lokacin da aka gudanar da zaben fidda gwani, Modibbo ya na aikin yi wa kasa hidima, bai kammala ba.

Babbar Kotu a karkashin Mai Shari’a Abdul’aziz Anka ya  ce mai kara ya gabatar da hujjojin da su ka gamsar da kotun cewa bai kamata APC ta tsaida Modibbo a matsayin dan takarar ta ba.

Wannan hukunci bai yi wa wanda ya zo na biyu dadi ba a zaben fidda-gwanin na APC, inda ya garzaya kotun daukaka kara domin bin bahasi.

Kotun Daukaka Kara kuma ta yanke hukuncin cewar Mustapha Usman ne ya kamata ya maye gurbin Modibbo.

Amma shi kuma Modibbo sai ya shigar da kara a Kotun Koli domin neman kada a kwace nasarar da ya yi.

Sai dai kuma a hukucin da Kotun Koli ta yanke ta ba da nasarar ce ga dan takarar PDP a zaben Majalisar Tarayya, wanda ya zo na biyu, ba ga dan takarar zaben fidda-gwani na APC da ya yi na biyu ga zaben fidda-gwani ba.

Dan takarar PDP mai suna Jafar Suleiman ne dai ya zo na biyu a babban zaben da aka gudanar a watan fabreru.