✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun koli ta tabbatar da sahihancin takarar Abba Kabir Yusuf

Kotun Koli da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da daukaka karar da Ibrahim Al’amin Little ya yi yana kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara…

Kotun Koli da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da daukaka karar da Ibrahim Al’amin Little ya yi yana kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara ta Kaduna wanda ya tabbatar da sahihancin zaben fidda gwani da Jam’iyyar PDP ta yi a Jihar Kano inda ta tsayar da Injiniya Abba K. Yusuf a matsayin dan takararta.

Alkalan kotun karkashin jagorancin Babban jojin na Kasa Mai shari’a Tanko Muhammad sun bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne saboda mai kara ya gaza bayyana hujjoji musamman ma dai ganin cewa a cikin kunshin tuhumar ba a sanya sunan Abba Kabir Yusuf a jerin wadanda aka yi karar ba.

Barista Bashir Tudun Wuzurci shi ne lauyan Jam’iyyyar PDP ya bayyana cewa Abba Kabir Yusuf shi ne halastaccen dan takara na Gwamna a Kano karkashin tutar Jam’iyyar PDP.