Daily Trust Aminiya - Ganduje ya sake kayar da Abba Giga-gida
Subscribe

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje

Ganduje ya sake kayar da Abba Giga-gida

Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da Abdullahi Umar Ganduje a matsayin halattaccen gwamnan jihar Kano.

Duka alkalan kotun guda biyar sun yi watsi da karar da Abba Kabir Yusuf da jam’iyyarsa ta PDP suka daukaka saboda rashin cikakkun hujjoji.

Abba ya nemi kotun da ta yi watsi da nasarar da Ganduje ya samu a zaben na watan Maris din 2019, yana mai cewa ba a bi ka’ida wurin soke kuri’un da aka kada a wasu mazabu, abin da ya kai ga sake zabe a cikinsu.

Alkalan kotun sun hada da Sylvester Ngwuta, Kudirat Kekekere-Ekun, Olukayode Ariwoola, Amina Augie da kuma Uwani Abba-Aji.

Ita dai jam’iyyar PDP da dan takararta Abba Kabir, sun shigar da kara ne suna kalubalantar zaben musamman matakin da hukumar zabe ta dauka na soke kuri’un da aka kada a mazabar Gama.

Sun ce an yi hakan ne ba bisa ka’ida ba – lamarin da ya bai wa Ganduje damar lashe zaben da aka karasa.

Sai dai Ganduje da APC sun nemi kotun da ta yi watsi da bukatar Abba da PDP, suna masu cewa jami’in zabe ne ya soke kuri’un kamar yadda doka ta tanada.

A makon da ya gabata ne kotun ta soke zaben Emeka Ihedioha na jam’iyyar PDP sannan ta nada Hope Uzodinma na APC duk da cewa Iheordia ne ya yi nasara a kotuna biyu na farko.

Wannan ya sa wasu ‘yan PDP a Kano samun kwarin gwuiwar cewa su ma za su samu nasara.

An dade ana kai ruwa-rana kan sakamakon zaben da kuma shari’ar da aka yi.

Masu lura da al’amura na ganin watakila hukuncin kotun ya kawo karshen turka-turkar siyasar da aka shafe dogon lokaci ana yi a jihar ta Kano.

texem
More Stories