Da Dumi Dumi

Kotun Koli ta tabbatar da zaben Gwamnan Bauchi

Gwamna Jihar Bauchi Bala Mohammed
Gwamna Jihar Bauchi Bala Mohammed

Kotun Koli ta tabbatar da zaben Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, bayan ta yi watsi da daukaka kara da tsohon Gwamnan Jihar Abubakar Muhammed ya gabatar.

Jagoran alkalan, Mai shara’a Dattijo Mohammed ya ce Kotun Kolin ba ta gamsu da bayanan dan Abubakar Muhammed da Jam’iyyar APC.

Shi dai Sanata Bala Muhammed na Jam’iyyar PDP ya doke abokin takararsa Abubakar Muhammed na Jam’iyyar APC, wanda a lokacin shi ne mai gwamna mai ci a zaben 9 ga watan Maris na bara.

Share