✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Koli ta tabbatar da zaben Tambuwal

Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da Aminu Waziri Tambuwal a matsayin halattaccen gwamnan jihar Kano. Duka alkalan kotun guda biyar sun yi watsi da karar…

Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da Aminu Waziri Tambuwal a matsayin halattaccen gwamnan jihar Kano.

Duka alkalan kotun guda biyar sun yi watsi da karar da Ahmed Aliyu da jam’iyyarsa ta APC suka daukaka saboda rashin cikakkun hujjoji.

Ahmed ya nemi kotun da ta yi watsi da nasarar da Tambuwal ya samu yana mai cewa shi ne ya lashe zaben.

Tun da farko kotun ta tabbatar da nasarar Abdullahi Umar Ganduje a matsayin zababben gwamnan jihar Kano, inda ta yi watsi da karar da Abba Kabir Yusuf ya daukaka.

Alkalan kotun sun hada da Sylvester Ngwuta, Kudirat Kekekere-Ekun, Olukayode Ariwoola, Amina Augie da kuma Uwani Abba-Aji.

Tun da farko lauyan APC Alex Izinyon (SAN), ya nemi kotun da ta soke zaben Tambuwal saboda acewarsa gwamnan ya kasa nuna shaidun da suka tabbatar da cewa ya samu kuri’u 342 da suka ba shi damar lashe zaben.

Shi dai Aliyu ya samu kuri’u 511,661 yayin da Tambuwal ya samu 512,002  bayan da aka kammala karashen zaben.

Sai dai lauyan PDP da Tambwal, Emmanuel Ukala (SAN) da Muyiwa Akinboro (SAN), sun nemi kotun da ta yi watsi da karar.

Sun bayyana cewa sun nuna duk shaidar da ake bukata da ta tabbatar da cewa Tambuwal ne ya lashe zaben.

“Kotun Koli ba za ta sauya hukuncin da kotunan baya suka yanke ba idan dai ba an tabbatar da cewa an yi kuskure ba ne,” a cewar Akinboro.

An dade ana kai ruwa-rana kan sakamakon zaben da kuma shari’ar da aka yi.

Masu lura da al’amura na ganin watakila hukuncin kotun ya kawo karshen turka-turkar siyasar da aka shafe dogon lokaci ana yi a jihar ta Sokoto.