✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Koli ta yi watsi da karar Atiku

Akwai masu tarnaki ga shari’a – Atiku Ya kamata Najeriya ta kara gaba  – Buhari Dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyar PDP a zaben da…

  • Akwai masu tarnaki ga shari’a – Atiku
  • Ya kamata Najeriya ta kara gaba  – Buhari

Dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyar PDP a zaben da ya gabata,  Alhaji Atiku Abubakar ya ce wadansu tsirari suna yi wa bangaren shari’a tarnaki.

A  shekaranjiya Laraba  ce Kotun Koli ta yi watsi da karar da Atiku Abubakar ya shigar yana kalubalantar nasarar Shugaba Buhari a zaben da ya gabata.

Atiku ya mayar da martani ne jim kadan bayan Kotun Kolin ta yanke  hukuncin korar karar da ya shigar wanda hakan ya tabbatar wa Shugaba Muhammadu Buhari nasara a zaben bana.

Sai dai a nasa bangaren Shugaba Buhari ya bayyana gamsuwarsa game da hukuncin da kotun ta yanke na tabbatar masa da zaben da ya lashe a bana.

Atiku Abubakar dai zai cika shekara 73 a ranar 25 ga Nuwamban nan. Shi da Jam’iyyar PDP ne suka daukaka karar zuwa kotun bayan da Kotun Sauraron Karar Shugaban Kasa a karkashin Mai shari’a Muhammad Garba, ta yanke hukuncin da ya bai wa Shugaba Buhari nasara a zaben da aka gudanar  a watan  Fabrairun bana.

Sauran wadanda aka kai karar sun hada da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da Jam’iyyar APC.

A lokacin da ake yanke hukuncin korar karar, a shekaranjiya Laraba alkalai 7 da suka zauna domin yanke hukuncin bisa jagorancin Babban Jojin Najeriya Mai shari’a Tanko Muhammad ba a dauki lokaci ba suka yanke hukunci inda suka nuna daukaka karar ba ta da tushe balle makama.  Sai dai alkalan sun ce za su yi cikakken bayani nan gaba kadan game da hukuncin da suka yanke.

Mai shari’a Tanko ne ya karanta hukuncin da kotun ta yanke, inda ya  ce sun shafe kusan mako biyu suna nazari a kan shari’ar da aka gudanar da muhawarar da aka tafka daga dukkan bangarorin biyu a kotun baya. Ya ce a nan gaba za su bayar da dalilin da suka sa suka kori karar ta Atiku.

Ragowar  alkalan sun hada da Bode  Rhodes Bibour da Olukayode Ariwoola da John Inyang Okoro da Amiru Sanusi da Ejembi Eko da kuma Uwani Abba Aji inda dukkansu suka amince da hukuncin.

A hirar da BBC ya yi da Atiku ya ce hankoron da yake yi na zama shugaban kasa a zaben bana yanzu ta zo karshe.