✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Kolin Amurka ta hallata aure tsakanin shakikai bayan shekara 10 ana shari’a

Wani mutum a birnin New Jersey na Amurka da         kanwarsa, sun yi nasara a wata shari’a da Kotun Kolin Kasar ta yanke bayan doguwar…

Wani mutum a birnin New Jersey na Amurka da         kanwarsa, sun yi nasara a wata shari’a da Kotun Kolin Kasar ta yanke bayan doguwar shari’a, cewa za su iya auren juna. Shi ne hukunci na farko da ya halatta aure tsakanin ’yan uwa kuma shakikai, a Amurka.

A hukunce-hukuncen da aka yanke guda hudu zuwa biyar, alkalan kotun biyar sun yi ittifaki a kan daukaka karar da James mai shekara 41 da kanwarsa Bictoria, mai shekara 38, bayan shafe shekara 10 suna tafka shari’a don a kyale su su auri juna duk da kasancewarsu uwa daya uba daya. ’Yan uwan biyu, sun yi ta murna, suna cewa sun yi haka ne domin miliyoyin Amurkawa shakikai da suke mu’amala irin ta ma’aurata, alhali iyayensu daya ne; amma suke tsoron fitowa fili su bayyana. Sun soki gwamnati game da barnata kudaden Amurkawa masu biyan haraji wajen kalubalantar wannan mataki nasu ta fuskar shari’a.

“Tun farkon samuwar dan Adam ake mu’amalar aure tsakanin muharramai. Idan da har Annabi Adamu da Hauwa’u, ba su yi hakan ba, to kuwa da mun wayi gari babu wani dan Adam a yau.” James ya gaya wa manema labarai, bayan nasarar da suka yi mai cike da tarihi.

Lauyan da ya wakilci iyalan gidan Banes, Julianne Grey, ya nace cewa, haramta aure a tsakanin shakikai ko muharramai; alhali a daya gefen kuma an halatta aure tsakanin ’ya’yan ’yan uwa a Jihar New Jersey, rashin hankali ne kuma nuna wariya tsantsa.

“Me ya sa za a kyale ni na tare da ’yar dan uwan iyayena; amma a hana ni tarewa da ’yar uwata? Babu hankali a ciki, ko kadan,” Kamar yadda James ya yi suka a wajen kotun.

Su dai wadannan ma’aurata da a baya suke iya fuskantar daurin shekara 15 a kurkuku; sun ce yanzu suna shirin kafa wani gagarumin iyali, kuma su yi walwala cikin sabon ’yancin da suka samu.

“Mun kasance a kullum muna da burin ganin mun kafa babban iyali, amma yanzu mafarkinmu ya zama gaskiya.” Bictoria Banes, ta bayyana, ta kuma fada wa manema labarai cewa ‘Ita fa tana dauke da juna biyu a halin yanzu; kuma tana tsammanin haihuwar ’yan biyu.’

A baya-bayan nan dai dokokin Jihar New Jersey sun amince da aure ne a tsakanin ’ya’yan ’yan uwa kawai; amma bayan wannan hukunci na Kotun Kolin, yanzu jihar ta kasance jiha daya a fadin Amurka da ta sahale aure tsakanin ’yan uwan juna.

Tuni dai aka fara samun tofin Allah tsine kan wannan  hukunci hatta a tsakanin masu ganin wayewar Amurka.